Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Published

on

Gamayyar masu shiryawa da kuma jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood sun karrama sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Habu Ahmed Sani.

Yayin wata ziyarar nuna goyon baya da kuma karawa kwamishinan kwarin gwiwa da ‘yan Film din suka kai masa karkashin jagorancin Alasan Kwalli, a shalkwatar rundunar ‘yan sanda dake unguwar Bompai.

Hoto a yayin ziyarar

‘Yan Film din sun hada da wakilan kungiyar jarumai, masu shirya fina-finai da masu daukar nauyi da kuma masu daukar hoto.

A yayin taron dai jaruman masana’antar Kannywood sun karrama kwamishinan da lambobin yabo na musamman.

Da yake jawabi a yayin taron Kwamishinan’Yan sanda na jihar Kano CP. Habu Ahmed Sani wanda ake yiwa lakabi da Kalamu Wahid ya bayyana cewa a shirye yake tsaf domin hada kai da ‘yan Film wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Kwamishinan yayi kira da ‘yan Film din da su baiwa ‘yan sanda gudummuwa ta hanyar wayar da kan al’umma kan irin ayyukan da ‘yan sanda keyi wajen kyautata tsaro da zaman lafiyar al’umma.

Daga cikin ‘yan Film da sukayi jawabi a wurin taron sun hada da Alasan Kwalli, Baba Karami, Mudassir Haladu, Halima Atete, Teema Makamashi, Dan’azumi Baba, Baba Ari da sauransu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!