Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

‘Yan Kannywood sun fara komawa aiki bayan kullen Corona

Published

on

Bayan shafe watanni cikin dokar zaman gida sanadiyyar cutar Corona, yanzu haka tuni jama’ar masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood suka ce sun fara komawa ci gaba da gabatar da ayyukan su kamar yadda su ka saba a baya.

Mai shirya fina-finan hausa, Aminu S. Bono da kuma jarumai da suka hada da Amal Umar, da Amina Lawan wadda aka fi sani da Raliya ta shirin dadin kowa da kuma fitaccen mawakin nan Ishe Baba sun shaidawa Freedom Radio cewa tuni suka ci gaba da ayyukan su na daukar fina-finai da waka bayan da hukumomi suka sassauta dokar kulle.

Sai dai mai bada umarni a masana’antar ta Kannywood Yaseen Auwal ya bayyanawa Freedom Radio cewa, zaman kulle da aka yi a gida, babu wadanda ya fi yiwa illa kamar, ‘yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, musamman wajen karya musu tattalin arziki.

Karin labarai:

Addu’o’I sun fara nasara a Kannywood

Mahaifiya ta ce ta karfafamin gwiwar shiga Kannywood – Raliya

To amma daya daga cikin masu shiryawa da daukar nauyin fina-finan hausa Mubarak Abba ya zayyanawa Freedom Radio wasu matakai da ya ce, idan har an bi su babu shakka za a samu masana’antar ta farfado nan bada jimawa ba.

Na farko, Mubarak ya ce, gwamnati tayi duba na tsanake, wanda zai kalli kowane bangare domin karfafa musu gwiwa wajen farfadowa, sannan ‘yan film su rage yawan fina-finan da suka shirya yi, a maimakon hakan su mayar da hankali wajen yin fina-finai kadan masu inganci.

Ya kuma ce, baya ga hakan, sai ‘yan film sun rage kashe kudade domin su samu bai wa sana’arsu kulawa ta kudi, sannan gwamnati ta duba wuraren haraji ta dagewa masu shirya fina-finai.

A karshe Mubarak Abba ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara taimaka musu waje magance matsalar satar fasaha wadda ta yi kaka gida a masana’antar.

Freedom Radio ta tuntubi shugaban hukumar tace fina-finai na Kano, Isma’il Na’abba Afakallah wanda ya ce, yanzu haka tuni shirye-shirye, sun yi nisa wajen ganin an samar da tsarin da zai karfafi gwiwar ‘yan masana’antar film wajen inganta sana’ar su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!