Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mahaifiya ta ce ta karfafamin gwiwar shiga Kannywood – Raliya

Published

on

Matashiyar jarumar nan Amina Lawan wadda akafi sani da Raliya a shirin wasan kwaikwayo na Dadin Kowa ta bayyana cewa mahaifiyarta ce ta bata kwarin gwiwa domin shiga a dama da ita a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Raliya ta bayyana hakan ne yayin zantawar da tayi da Freedom Radio inda tace “Ina sha’awar na shiga harkar fina-finan Hausa domin nima na bada gudummuwa ta wajen wayar da kai da ilimantar da al’umma, kuma na samu cika burina kasancewar mahaifiya ta tana cikin iyaye a masana’antar, don haka ta karfafamin gwiwa ba tare da wani cikas ba”.

Mahaifiyar jaruma Amina ita ce Hajiya Halima Lawan wadda akafi sani da Sabuwa matar Ayuba mai gadi a shirin Dadin Kowa.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da wasu al’umma ke sukar jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa da cewa mafi yawa basu cika amincewa ‘ya’yan su su shigo a dama dasu a masana’antar ba.

Shekaru hudu kenan da matashiyar jarumar Amina Lawan mai shekaru 20 ta fara taka rawa a fina-finan Hausa, inda take Film da kuma waka.

Sai dai Tauraruwar Jarumar ta haska ne bayan fitowar ta a shirin Dadin Kowa wadda take cikin manyan jarumai da jama’a ke tausayawa kasancewar ta fito a cikin wahala.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!