Rahotonni
Rahoto : ‘Yan KAROTA na kwashe mana kaya da cin zarafin mu – ‘Yan kasuwar ‘Yankaba
Daga Abdulkarim Muhammad Tukuntawa
Masu gudanar da sana’ar sayar da kayan gwari a kasuwar ‘yan Kaba a nan Kano sun koka bisa yadda jami’an hukumar Karota ke shigowa kasuwar suna kwashe musu kaya tare da cin zarafinsu.
Wannan al’amari dai a cewar ‘yan kasuwar, yana ci musu tuwo a kwarya duk da cewa wajen da aka umarcesu su rika ajiye kayansu a nan su ke yi.
Da safiyar jiya Laraba ne rikici ya barke tsakanin jami’an hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Kano KAROTA da wasu matasan ‘yan kasuwar sayar da kayan gwari dake ‘Yankaba bayan da jami’an Karota suka shigo kasuwar tare da kwashe kayayyaki, wadanda suka ce an zuba su a kan titi.
Ya mutsin dai ya durkusar da harkokin kasuwanci a kasuwar a jiya, inda ‘yan kasuwar suka zargi ‘yan KAROTA da kawo musu cikas a harkokinsu.
Umar Ibrahim shine shugaban kungiyar masu sayarda kayan gwari na jihar Kano, ya ce, abunda jami’an Karota su kayi a kasuwar yana kan doron doka kuma suna goyan bayan hakan kasancewar duk wanda ya karya doka doka zatayi aiki akansa.
Shugaban kungiyar Umar Ibrahim ya kuma nesanta ‘yan kasuwar da tayar da waccen rikici.
Munyi kokarin jin tabakin shugaban hukumar Karota ta Jihar Kano Baffa Babba Danagundi domin jin hanzarin hukumar amma hakan bai yiwuba kansancewar mun kiran shi a waya amma bai dauka ba kuma mun aike masa da sakon karta kwana amma kawo yanzu babu amsa.
‘Yan kasuwar sunyi kira ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya sanya baki don kawo karshen irin cin zarafin da jami’an hukumar Karota keyi musu.
You must be logged in to post a comment Login