Connect with us

Labarai

 ‘Yan kasashen waje 840,000 ne wa’adin bizarsu ya kare a Nijeriya –  Gwamnati

Published

on

Ministan harkokin cikin gida na Nijeriya Olubunmi Tunji Ojo ya ce ‘yan kasashen waje sama da 840,000 ne wa’adin bizarsu ya kare a kasar, kuma ba su dauki matakin sabunta ta kk ficewa ba.

 

Ministan ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce mutanen sun kasance ‘yan kasashen duniya daban-daban.

 

Wannan ya zo a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan wata yarjejeniya da Nijeriya ta kulla da kasar Birtaniya kan hadin gwiwa a fannin shige da fice, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Sai dai ministan ya jaddada cewa, Nijeriya ba za ta amince da karbar daurarru ko masu laifi daga wata kasa ba, sannan babu batun bayar da mafaka ga masu gudun hijira daga ketare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!