Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

‘Yan kasuwa sun nemi El-rufa’i ya bude kasuwanni

Published

on

‘Yan kasuwa a jihar Kaduna sun roki gwamnan jihar Malam Nasir El-rufa’i kan ya bude musu kasuwannin jihar domin ci gaba da kasuwanci.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na jihar Kaduna Alhaji Shehu Ibrahim Daudawa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilin Freedom Radio Abdullahi Ibrahim Gambo.

Daudawa ya ce, yanzu haka sun yi zama na musamman da hukumar raya kasuwanni ta jihar Kaduna domin ganin an samu matsaya ta yadda gwamnati zata amince su ci gaba da bude dukkanin kasuwannin jihar duba mawuyacin halin da ‘yan kasuwa suka shiga sanadiyyar rufe kasuwannin.

A ranar Laraba 10, ga watan Yunin da ya gabata ne, gwamna El-rufa’i ya sassauta dokar kulle a jihar, sai dai bai amince da ci gaba da bude kasuwanni ba, wanda ya zamowa ‘yan kasuwar tamkar ta leko ta koma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!