Connect with us

Kaduna

Zafin ciwo ya sanya wani mutum fede cikin sa da wuka a Kaduna

Published

on

Wani magidanci a jihar Kaduna ya fede cikin sa da wuka sanadiyyar zafin cutar gyambon ciki wato (Ulcer) dake damun sa.

Wannan al’amari dai ya faru ne, a garin Lere dake jihar Kaduna inda magidancin mai suna Hashim Muhammad ke fama da cutar ulcer wanda zafin ciwon ta ya sanya, yayi amfani da wuka wajen fede cikin sa.

Wakilin Freedom Radio Haruna Ibrahim Idris ya samu tattaunawa da Aisha Muhammad wadda kanwa ce ga mutumin, wadda ta ce ya jima yana fama da cutar ta ulcer, sai dai a wannan karon abin ya zo da zafi.

Yanzu haka dai Hashim Muhammad na kwance a gadon babban asibitin garin Lere, cikin mawuyacin hali, inda yake samun kulawar jami’an lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!