Labaran Kano
‘Yan kasuwa sunyi sulhu da barawon waya
Jami’an kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Beirut dake nan Kano sun cafke wani matashi mai suna Johnson sakamakon satar sabuwar wayar hannu da yayi a kasuwar.
Tun a jiya Asabar ne dai matashin wanda yazo tun daga garin Calabar na jihar Cross River ya fara zagaye sassan kasuwar.
Inda a yau kuma matashin ya aikata dabi’ar dan hali, har yayi awon gaba da wayar hannu, sai dai bayan da jami’an kasuwar suka cafke shi, ya sanar dasu cewa hakika ba da son ransa ya aikata wannan laifin ba, domin kuwa yana da wata cuta ce wadda da zarar ya ga kayi wasarerai da kayanka to zai yi awon gaba dashi.
Jami’in hurda da jama’a na kungiyar masu sayar da wayoyi na kasuwar ta Beirut Jamilu Malam Gama ya shaidawa Freedom Radio cewa mai laifin ya rubuta takarda da hannunsa kan abinda ya aikata, da kuma neman afuwa, a don haka suka sallameshi da sharadin ba zai kara aikata wannan laifi ba.
Sai dai Freedom Radio ta tuntubi kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Kano, DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa inda ya bayyana mana cewa basu samun labarin faruwar wannan al’amari ba, kuma suna kira ga al’umma kan duk sanda irin wannan abu ya faru kuma ake da bukatar sulhu, to a tabbatar anyi shi a gaban hukuma, domin gudun abinda zaije yazo.
Allah ya kyauta.
Rubutu masu alaka:
Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna
Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood
An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne
Amarya ta haihu bayan wata hudu da Aure