Labarai
Yan Kwankwasiyya sun maka Garba Kore a Kotu

Wasu yan siyasa da ke tsagin Kwankwasiyya, sun maka ɗan siyasar nan na jam’iyyar adawa ta APC a Kano Garba kore Dawakin Kudu a gaban kotu bisa zarginsa da bata wa gwamna Abba Kabir Yusuf suna.
Masu karar sun haɗa da: Mai bai wa gwamna shawara na a bangaren yada labarai Alhajiji Nagoda da kuma Sakataren kungiyar NNPP Kwankwasiyya Abba gida-gida watau Ali Gyara Hausawa inda suka shigar da karar a gaban babbar kotun shariar Musulunci da ke Kofar Kudu karkashin jagorancin mai sharia Ustaz Ibrahim Sarki yola.
Ali Gyara shi ne ya bayyana wa kotu daawarsu, har ma ya kara da cewa su na kararsa ne sakamakon zargin ya shiga wata kafar yada labarai tare da cewa Babu abinda zai Hana gwamna Abba Kabir shiga wuta sai dai idan bai mutu ba, Haka kuma ana zarginsa da cewa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso Ɓarawo.
Bayan Jin daawarsu kotu ta waiwayi lauyan Wanda ake kara Barista Mustapha Idris inda Yazo da tawagar lauyoyi guda biyar, inda ya shaida wa kotu cewar sun ji karar amma akwai rashin hurumun kotu wajen sauraron shari’ar, don haka ya roki kotun da ta basu wani lokaci za su kawo mata hujjojinsu a rubuce.
Daga bisani Kotun ta sanya ranar 28 ga watan nan da muke ciki na Mayu domin Jin bayanin su.
You must be logged in to post a comment Login