Connect with us

Labaran Kano

‘Yan mata sun cafke barawon kayan lefe a Kano

Published

on

Wasu gun-gun ‘yan mata sun cafke wani matashi da suke zargi da satar lefen ‘yar uwar su a unguwar Sheka Rigar Kuka dake nan Kano.
Wasu daga cikin ‘yan matan da sukayi rubdugu wajen cafke matashin sun shaidawa Freedom Radio cewa matashin ya kutsa cikin gidan su, tare da satar atamfofi da leshi cikin akwatun kayan lefe.

‘Yan matan sun lakadawa matashin dukan tsiya sannan suka mika shi ga jami’an sintiri na yanki.

Karin labarai:

Hisbah ta kama mai yiwa mata kunshi

‘Yan kasuwa sunyi sulhu da barawon waya

Shi ma a nasa bangaren matashin da aka cafke ya shaidawa Freedom Radio cewa babu shakka ‘yan matan sun ci zarafin sa, sun kuma keta masa haddi wajen yi masa duka da tara masa jama’a, don kawai ya saci kayan lefen su.

Yunusa Sulaiman Sheka shi ne kwamandan jami’an sintiri na yankin unguwar Sheka ya shaidawa wakilin mu Yusuf Ali Abdallah cewa yanzu haka matashin yana hannunsu inda suke shirin mika shi ga ‘yan sanda.

Cikakken labarin zai zo muku a shirin Inda Ranka na daren yau, da misalin karfe 9:30 na dare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!