Connect with us

Labaran Kano

Wasu matasa sun yi kokarin shigar da kwaya gidan yarin Kano

Published

on

Hukumomin gidan ajiya da gyaran hali na Goron Dutse dake nan Kano, sun cafke wasu matasa biyu da ake zargi da yunkurin shigar da kwaya gidan yarin.
Wakilin mu Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito mana cewa da safiyar yau ne matasan suka je domin ziyara dauke da kabakin abinci ciki har da gurasa.
Sai dai a binciken da jami’an gidan yarin suka yi, sun gano kunshin kwayoyin maye makare a tsakiyar gurasa.
Kakakin hukumar lura da gidajen ajiya da gyaran hali na jihar Kano DSC. Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar al’amarin, inda ya ce suna cigaba da bincike da zarar sun kammala za su mika su kotu.

Cikakken labarin zai zo muku a shirin Inda Ranka na daren yau, da karfe 9:30pm.

Karin labarai:

An garkame Sadiya Haruna a gidan yari

An cafke budurwa na yunkurin shigar da kwaya gidan Kurkukun Kurmawa na Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!