Labarai
Yan matan Kebbi da aka kubutar suna cikin koshin lafiya – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta sanar da kubutar da daliban sakandiren ‘yan mata da ke garin Maga a jihar Kebbi su ashirin da hudu.
Cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya yaba wa kokorin jami’an tsaron kasar kan kubutar da daliban.
A wani bidiyo da aka wallafa na yaran bayan kubutar da su, an gansu cikin wata motar bas tare da jami’an tsaro, suna bayyana sunayensu daya-bayan daya.
A makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka far wa makarantar tare da sace daliban da kashe malami guda.
You must be logged in to post a comment Login