Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun kubutar da 1 daya daga cikin sauran daliban Chibok

Published

on

Rundunar sojin Nijeriya  karkashin dakarun bataliya ta 114 da ke aiki a karamar hukumar Goza ta jihar Borno, ta samu nasarar kubutar da karin daliba 1 cikin yan matan Chibok da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su a shekarar 2014.

Dakarun sun samu nasarar kubutar da dalibar mai suna Hauwa Malsa yar kimanin shekara ashirin da shida a ranar 21 ga watan Afrilun da ya gabata tare da jaririyarta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, daliba Hauwa ta auri guda daga cikin mambobin kungiyar ta Boko Haram mai suna Salman wanda shi ne mai daukar hoton tsohon shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, wanda daga bisani ta sake auren malam Muhammad, bayan rasuwar Salman a yanking tafkin Chadi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!