Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Najeriya miliyan 30 sun yi rijistar fita daga kangin talauci – Buhari

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ce ta yiwa ‘yan Nijeriya sama da miliyan 30 rajistar karkashin shirin nan na fitar da mutane miliyan 100 daga talauci a shekaru 10 masu zuwa.

Babban sakatare a ma’aikatar kula da jin kai da kare abkuwar ibtila’I da ci gaban al’umma Alhaji Bashir Alkali ya bayyana hakan yayin gudanar da wani taro a birnin tarayya Abuja.

Ya ce a karkashin shirin ma’aikatar ta samar da tsarin bada tallafi da hadin guiwar bankin Duniya don rage talauci farfado da tattalin arziki a Najeriya.

A cewar sa shirin zai fara ne daga matakin tarayya zuwa jihohi, har zuwa matakin kananan hukumomi, abin da ke nuna rukuni uku na gwamnatoci za su ci gajiyar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!