Connect with us

Kiwon Lafiya

‘yan Najeriya na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasa da na yan majalisu

Published

on

A yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC za ta fara tattara sakamako zabe a yau yan Najeriya na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasa da na yan majalisu da aka kada tun a ranar Asabar din da ta gabata.

A cewar hukumar zaben da misalin karfe 11 na safiyar yau Litinin ne za a fara sanar da sakamakon zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a hukumance.

Yayin da hukumar ta INEC ke cigaba da aikin tattara sakamakon zabukan da aka gudanar, a jiya Lahadi an bai wa jama’a damar kada kuri’unsu a wasu mazabu da ke kananan hukumomi 10 na jihar Zamfara, inda jama’a suka kasa yin zaben a ranar Asabar.

Haka kuma INEC ta ce za ta bayyana sabbin ranakun da za a sake gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilai da dattijai, a wasu yankuna na jihohin Anambra da Rivers da Lagos sakamakon rikicin da aka samu da kuma sace akwatinan zabe.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!