Labarai
‘Yan Najeriya za su yi mamaki idan na bayyana masu hannu a sace daliban Jangebe – Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce ‘yan Najeriya za su yi matukar mamaki idan suka ji sunayen mutanen da ke da hannu wajen sace daliban makarantar sakandiren mata ta Jangebe da ke jihar a ranar juma’a 26 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
Bello Matawalle ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya goma sha bakwai na jihar wadanda suka kai masa ziyarar jaje a fadar gwamnatin da ke birnin Gusau.
Gwamnan na Zamfara ya ce al’ummar kasar nan za su sha mamaki sosai matukar ya bayyana mutanen da ke da hannu wajen sace daliban.
Da ya ke gabatar da jawabi sarkin Anka kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Alhaji Attahiru Anka, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da sace-sacen dalibai, yana mai shawartar gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen shawo kan matsalar.
A ranar juma’a da ta gabata ne dai ‘yan bindiga suka sace dalibai mata a makarantar sakandiren Jangebe da ke yankin karamar hukumar Talata Mafara.
You must be logged in to post a comment Login