Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kalubale

‘Yan Nijeriya sun shiga rudani kan ranar daina amfani da tsoffin kudi

Published

on

A gobe juma’a ne wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudi zai cika bayan da babban bankin kasa CBN ya sanar da karin wa’adin kwanaki goma, bayan da wa’adin farko na watan janairu ya cika.

Sai dai ga dukkan alamu, akwai tufka da warwara kan takamaiman ranar daina amfani da tsoffin kudin.

Domin jin cikakken rahoton danna alamar sauti.

Rahoton: Hafsat Ibrahim Kawo.

Kotun kolin kasar nan da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin dakatar da gwamnatin tarayya daga daina amfani da tsoffin takardun kudi da ta tsara farawa daga 10 ga watan Fabrairun nan da muke ciki.

Tawagar alkalan kotun, karkashin jagorancin  John Okoro, ta shaidawa kotun cewa sun shigar da karar ne biyo bayan korafe–korafen da gwamnonin jihohin Arewacin kasar nan da suka hadar da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka yi kan matakin, baya ga la’akari da matsi da al’ummar Najeriya ke ciki.

To sai dai gwamnatin Tarayyar ta bukaci Kotun Kolin kasar ta janye umarnin da ta yi a ranar Laraba da ke yin watsi da dokar daina amfani da tsaffin takardun kudi na Naira, hukuncin da ke nuna dakatar da wa’adin Juma’an nan 10 ga watan Fabarairu da babban bankin kasar CBN ya kayyadewa al’umma na ganin sun kammala mika tsaffin takardun kudinsu ga banki don karbar sababbi.

Wata wasika da lauyoyin ma’aikatar shari’ar Najeriyar Mahmud Magaji da Tijanni Gazali suka mika ga kotun kolin ta ruwaito Ministan shari’ar na cewa babu wasu kwararan hujjoji da zai sanya kotun har ta yanke hukunci kan karar da ke neman dakatar da wa’adin.

Tun farko dai gwamnaonin jam’iyyar APC 3 da suka kunshi na jihar Kogi Yahya Bello da na Kaduna Malam Nasir El Rufa’i da kuma na Zamfara Bello Matawalle ne suka shigar da karar gaban kotun koli da ke neman dakatar da bankin na CBN daga daina amfani da takardar kudin a daga ranar Juma’a 10 ga watan Fabarairu.

Sai dai Abubakar Malami ya bayyana cewa wadanda suka shigar da korafi kan lamarin basu da wasu kwararn hujjoji kan dalilin yin hakan, wanda ke nuna bukatar da ke akwai ga kotun kan ta janye hukuncin na ta.

A hannu guda kuma, Bankin bada lamuni na duniya IMF ya shawarci babban bankin kasa CBN da ya kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudi daga ranar 10 ga watan da muke ciki na Fabrairu, sakamakon irin wahalar da yan Najeriya ke sha wajen neman sabbin kudin.

Babban jami’in bankin IMF a nan Najeriya Ari Aisen ne ya bukaci hakan a yau Laraba cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, wa’adin karin kwanakin 10 da babban bankin kasa CBN ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kudin yayi kadan, a don haka akwai bukatar sake sanya wani sabon wa’adin.

A cewarsa, duk da karin wa’adin, har yanzu yan Najeriya na shan wahala wajen samun sabbin takardun kudin maimakon su samu cikin sauki, har ma ya nuna fargaba kan yadda matsalolin da ake fuskanta ka iya haifar da zanga-zanga da tashe-tashen hankula a fadin kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!