Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zaurawa sun yi bore kan hana zancen dare a Kano

Published

on

Zaurawa sun yi bore kan hana zancen dare a Kano

Wasu tarin zaurawa da ‘yan mata mazauna unguwar Gayawa a karamar hokumar Ungogo sun yi bore tare da nuna kin amincewa da wata sabuwar doka ta hana yin hirar dare tsakanin masoya da aka fi yinta daga bayan sallar Issha zuwa abinda ya sauwaka.

Dagacin yankin na Gayawa Alhaji Muntari Sale shi ne ya sanya dokar a baya-bayan nan da nufin kawo sauyi bisa yadda ake zargin ana fakewa da zancen domin cimma wata manufa.

Rahotonni sun bayyana cewa Dagacin garin ya kafa kwamitin da ya hadar da jami’an hukumar Hisba da na sintiri da sauran wasu mutane domin gudanar da aikin sintirin don hana zancen.

Wata matashiya mai suna Rabi’atu ta shaida wa Freedom Radio cewa sun ki amincewa da dokar ne saboda wasu daga cikin samarin nasu na zuwa ne daga nesa hakan ne ya sa daga sun fara zancen sai a korar musu su, ba tare da sun yi tattaunawar da suka fahimci juna ba.

A zantawar Freedom Radio da Dagacin ya ce sun hana zancen ne bayan karfe 09:00 na dare, yana mai cewa sun dauki matakin hakan ne sakamakon yadda wasu daga cikin masu zancen ke aikata badala da sunan zance.

Alhaji Muntari Sale, ya kuma bukaci iyayen da ake zuwa zance wajen ‘ya’yan su sanya masu zuwa zacen da su turo da magabatansu domin tsayar da maganar Aure matukar da gaske suke, domin ta haka ne za a tantance wadanda suke son yin auren na gaskiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!