Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda a Katsina sun kama wani matashi dake damfarar mutane ta hanyar kiran su a waya

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi mai suna Sadik Abubakar dake kiran mutane a waya yana razana su tare da karbar kudade a gurin su.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina Sp Gambo Isa ne ya bayyan hakan yayin da yake ganawa da mamema labarai.

Sp Gambo Isa ya ce matashin mai shekaru 18 dake zaune a kofar Guga dake cikin garin na Katsina, ya shahara wajen kiran mutane a waya domin karbar kudi a wajen su.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina ta bukaci al’umma da su rinka kai rahoton duk wani mutum da sukaga ya na aikata ba dai-dai ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!