Labarai
‘Yan sanda sun cafke dillalan miyagun kwayoyi sama da 1,000 a Kano
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama wadanda ake zargi dillalan miyagun kwayoyi ne da ‘yan banga dubu daya da dari biyar da tamanin da uku cikin watanni 8 da suka gabata.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Habu Ahmad ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna ya sanya wa hannu a yau Alhamis.
Sanarwar ta kara da cewar, kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana hakan ne lokacin da kungiyar da ke yaki da shan miyagun kwayoyi ta LSPADA ta kai masa ziyarar aiki a ofishin sa dake nan Kano.
Habu Sani ya ce, wadanda ake zargin dubu daya da dari biyar da arba’in da biyar talatin da takwas dillalan dake saida miyagun kwayoyi ne.
An dai kama su ne a a wurare daban-daban tsakanin watan Nuwanbar bara zuwa watan Yulin nan da muke ciki.
Da take jawabi shugabar kungiyar Hajiya Maryam Hassan ta yabawa rundunar ‘yan sandan jihar Kano saboda samar da tsaro a ciki da kewayen na Kano.
Hajiya Maryam Hassan ta kara da cewa, shirin gangamin wayar da kai na yaki da shan miyagun kwayoyi da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta fito da shi abun a yaba ne.
You must be logged in to post a comment Login