Labarai
Yan sanda sun cafke wasu matasa da ake zargi da satar Babur a Bauchi
Rundunar yan sandan jihar Bauchi, ta kama wasu matasa da ta ke zargin su da satar Babur kirar Boxer a garin Tenti Babba da ke jihar Plateau.
Mai magana da yawun rundunar SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar, ta ruwaito cewa, tun ranar sha shida ga watan Disamba nan da muke ciki ne wani mutum mai suna Haruna Maguwa, ya shigar da karar an sace masa babur din.
Haka kuma SP Ahmad Wakil, ya kara da cewa ‘yan sandan offishin Toro ne suka yi nasarar cafke wadanda ake zargin Yakubu Aminu da Abdul Lawal da kuma Buhari Abdullahi.
Ya kuma kara da cewa bayan kama wadanda ake zargin an same su da babur din inda rundunar ke ci gaba da gudanar bincike kuma za su gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abinda suka.
You must be logged in to post a comment Login