Labarai
Rundunar soja ta kasa ta ceto mutane daga hannun masu garkuwa
Rundunar sojan kasar nan kar kashin rudunar yaki ta Sahel Sanity ta ceto mutane 8 da aka sace aka yi garkuwa da su tare kuma da gano mukamai masu yawa a jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina.
Mukaddashin dake kula da sashin rundunar yaki na shalkwatar rundunar sojan kasar nan Birgediya janaral Benard Onyeuko ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
A dai ranar 6 ga wannan watan yulin babban hafsan sojan kasar nan Laftanal Tukur Buratai ya kaddamar da rundunar yaki ta Sahel Sanity a sansanin sojan na mussaman dake Faskari a wani bangaren na ranar tunawa da ‘yan mazan jiya.
Benard Onyeuko ya ce rundunar sojan asar nan ta kaddamar da rundunar ne da zummar yaki da ‘yan fashi makami da masu satar mutane sai an biya kudin fansa da satar shanu da sauran masu aikata miyagun laifuka.
You must be logged in to post a comment Login