Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda sun gurfanar da matashi bisa zarginsa da zambatar mata

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta gurafanar da wani matashi mai suna Salisu Shuaibu Hotoro a gaban kotu bisa tuhumarsa laifin damfara tare da zambatar ‘yan mata da kuma yi musu sata.

Bayan gurfanar da shi mai gabatar da kara Aliyul Abidin ya karanto masa kunshin tuhumar da ake masa, nan take kuma ya amsa tare da amincewa da zarge-zargen da ake masa.

Daga bisani kotun ta sanya ranar 9 ga watan nan da muke ciki domin yanke masa hukunci.

An dai zargi Salisu da laifin kai wata budurwa Otal in da ya dauke mata waya tare da sarkkokin gwal har ma da kudadenta.

Bayan faruwar hakan kuma tuni wasu matan suka fara zuwa ofishin ‘yan sanda suna ikirarin cewa su ma Salisun ya yaudare su tare yi musu sata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!