Labarai
‘Yan-sanda sun sanar da sace masu bauta sama da 160 a jihar Kaduna

Rundunar yan Sandan kasar nan ta tabbatar da cewa rahoton sace mutane a Kurmin Wali a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna gaskiya ne.
Hakan na cikin wata sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, CSP Benjamin Hundeyin ya sanya wa hannu
A cewar hukumar martanin farko na ‘yan sanda ba musanta lamarin ba ne, a’a martani da zai kwantar da hankalin jama’a ganin yadda al’umma suka shiga firgice kan faruwar almarin.
A ranar Litnin din da ta gabata ne rundunar yan sanda ta fitar da rahotan cewa ba gasiya bane sace mutanan sama da dari da sittin a jhar Kaduna kamar yadda wasu jaridun kasar nan suka wallafa.
You must be logged in to post a comment Login