Connect with us

Labarai

Yan sanda sun tarwatsa masu garkuwa da mutane a titin Funtua zuwa Gusau

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a kan titin Funtua zuwa Gusau a jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar na kasa ACP Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da  ya fitar.

sanarwar ta ruwaito cew,  jami’an rundunar sun yi nasarar dakile yunkurin sace wasu mutane goma da kuma direbobi biyu da fasinjoji takwas ba tare da an samu wadanda suka ji rauni ba.

Haka kuma, rundunar ta ce, jami’an nata sun yi artabu da ‘yan bindigar wadanda ke dauke da muggan makamai, lamarin da ya tilasta wa bata garin tserewa da raunukan harbin bindiga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!