Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sandan  Adamawa, sun cafke wani magidanci da  ya kashe tsohuwar  matarsa  

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ta kama wani magidanci mai suna Aminu Abubakar, dan shekaru 56, bisa zarginsa da dukan tsohuwar matarsa mai shekaru 38 da haihuwa wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ta .

Wanda ake zargin, mazaunin Lelewaji, ta karamar hukumar Yola ta Kudu ana zargin  ya kashe Nana Fadimatu kwana guda kafin auren ta da sabon mijin da zata aura.

SP Suleiman Nguroje shi ne mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Adamawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka cafke shi.

“Ya daki tsohuwar matar tasa ne sakamakon cewa yaji zata daura wani auren inda yanzu mun maida binciken zuwa babban sashin binciken  manyan laifuka idan har yanzu anan ana tattara bayanai.”

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!