Labarai
Yan sandan Plateau sun tabbatar da mutuwar mutane 3 a harin da yan bindiga a Pwomol

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Pwomol da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi da safiyar ranar Litinin.
Wadanda aka kashe din sun hada da matasa biyu da wani dattijo, yayin da wani mutum guda kuma ya jikkata.
Mai magana da yawun rundunar, Alabo Alfred, ya ce, jami’an tsaro sun kai ɗauki cikin gaggawa tare da fafatawa da maharan, lamarin da ya sa suka tsere zuwa dazuka.
Ya ƙara da cewa an kama wani da ake zargi, wanda yanzu haka ya ke tsare yayin da ake ci gaba da bincike domin cafke sauran.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bassey Ewah, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da shan alwashin cewa za a tabbatar da adalci kan lamarin.
Haka kuma, ɗan majalisar yankin, Dickson Y. Chollom, ya yi Allah-wadai da harin.
You must be logged in to post a comment Login