Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan ta’adda fiye da 400 sun mika wuya a Nassarawa – John Enenche

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su dari hudu da goma sun mika wuya ga rundunar sojojin kasar nan a jihar Nassarawa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa Manjo Janar john Enenche ya fitar, ta ce, mutane sun hada da mata da kananan yara kuma ‘yan kungiyar Darus Salam ne.

Manjo janar John Enenche ya kuma ce mutanen sun mika wuyar ne ga dakarun Operation Whirl Stroke wadanda aka turasu aikin tabbatar da tsaro a garin Uttu da ke yankin karamar hukumar Toto.

Haka zalika dakarun sun kuma kai samame wata masana’anta da ake  hada abubuwan fashewa tare da kwato na’urar jefa rokoki da buhuhunan takin zamani da gurneti na gargajiya da sauran wasu makamai da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!