Labarai
Yan ta’adda na cin karen su ba babbaka a Najeriya – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin shugaba Tinubu kan batun ceto ɗalibai mata da yan bindiga suka sace a Kebbi.
Atiku, ya ce, sako daliban ba wani abun da za a gabatar da shi ba ne a matsayin nasara, illa abunda ke nuna yadda tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a kasar nan.
A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya wallafa a yau Laraba, ya ce, bayyana cewa, lamarin na sake nuna wa al’umma cewa ƴan ta’adda na cin karensu babu babbaka a ƙasar nan, inda gwamnati ke ɓige wa da sanarwa maimakon dakile matsalar.
Jawabin nasa na zuwa ne a matsayin martani game da kalaman mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, a wata hira da ya yi, inda ya ce, hukumar tsaro ta DSS da sojoji sun gano inda masu garkuwa da mutanen suke, kuma bayan tuntuɓar su kuma aka kai ga nasarar cimma sako yaran ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
You must be logged in to post a comment Login