Labaran Wasanni
‘Yan wasan Nigeria na ci gaba da taka rawar gani a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai
Yan wasan Najeriya na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a ci gaba da fafata wasannin da gasar cin kofin zakarun nahiyar turai wato Champions league na kakar wasanni ta bana.
Daga kungiyar Slavia Prague dan wasa Peter Olayinka ya yi kokari matuka a wasan da kungiyar sa tayi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 2 da 1.
Dan wasa Stephen Odey, ya zura Kwallo daya tilo ga kungiyar sa ta RCK Genk dake kasar Belgium wacce ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 4 da 1.
Hakan ya biyo bayan kokarin ‘yan wasa irin su Emmanuel Dennis Bonaventure na kungiyar Club Brugge ita ma dake kasar Belgium, da dan wasa Victor Osimhen na kungiyar Lille Osc, dake kasar Faransa.
A dai gasar ta cin kofin a wasannin da aka buga da daren yau, kuma wasa na uku , shahararren dan wasan nan Lionel Messi na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ya bi sahun dan wasa Cristiano Ronaldo da Raul Gonzalez na kungiyar Real Madrid , wajen samun damar zura Kwallo a ragar kungiyoyi daban -daban har 33.
Haka kuma Messi ya kafa sabon tarihi na cin Kwallo a kowacce gasar na tsawon shekaru 15, wanda babu dan wasan da ya taba haka a tarihin gasar .
Dan wasan ya zura Kwallo a wasan yau da kungiyar sa ta fafata, da takwarar ta ta Salavia Prague , a rukunin F, minti 03 da fara wasan, wanda hakan ya bashi damar zura kwallayen ga kungiyoyi dai dai har 33.
kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tsallake rijiya da baya, bayan samun taimakon na’urar hoton Video na VAR, wanda ya kashe kwallon da kungiyar Ajax ta zura mata, hakan ya bata damar zura wa Ajax din Kwallo daya tilo har gida ta hannun dan wasa Mitchy Bacshuyi.