Connect with us

Labaran Wasanni

‘Yan wasan Tunisia biyu sun kamu da COVID-19

Published

on

‘Yan wasan kasar Tunisia biyu Ferjani Sassi da Seifeddine Khaoui sun kamu da cutar COVID-19.

An gudanar da gwajin cutar ne kan ‘yan wasan bayan fafatarwar su da Sudan a ranar Juma’ar makon jiya.

A dai gobe Talata ne Najeriya take shirin hadu da kasar ta Tunisia a wasan sada zumunta da ake gudanarwa a Austria.

Hakan zai zama kalubale ga tawagar ta Tunisia sakamakon kamuwar ‘yan wasan biyu, yayin da aka cire su daga cikin tawagar kasar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa,“Tuni dai aka zare ‘yan wasan biyu daga cikin wadanda zasu fafata da Najeriya a gobe Talata”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!