ilimi
Yana da kyau mawadata su kawowa jami’o’in kasar nan dauki- shugaban jami’ar Bayero
Shugaban jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas ya yi kira ga mawadatan kasar nan da su kasance masu tallafawa jami’o’i domin ganin an ciyar da ilimi gaba.
Farfesa Sagir Adamu Abbas ya bayyana hakan yayin a zantawarsa da Freedom Radio, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan batun yaye dalibai da jami’ar ke yi a makon nan.
Wanda ya ce dukkanin jami’o’in kasar nan, suna bukatar kudi ta yadda za su tafiyar da sha’anin koyo da koyarwa yadda ya dace, sai dai kuma dubada cewa gwamnati bazata iya daukar duka nauyin ba, masu hannu da shuni idan suka shiga lamarin, abubuwan zasu saukaka.’
A gobe asabar ne dai jami’ar za ta yaye daliban da suka samu kammala karatun digiri a fannoni da dama, inda ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin kasar nan za su halarci taron yayewar.’
Rahoton: Zahra’u Sani Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login