Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a wasu shagunan a Sharada

Published

on

Gobarar dai ta tashi ne da misalin 12 da rabi na rana a Dantata Plaza shaguna mai hawa daya a unguwar Sharada phase ll kusa da kwanar Freedom.

Wasu da suke makwabtaka da wadannan shagunan sun bayyana abubuwan da suke tunanin sune suka haddasa wannan gobarar.

Wandanda suka ce ‘yayi ake konawa a bayan shagunan, kamar wasa, sai wutar ta kamo ginin, Wanda kuma kafin su farga har wutar ta mamaye saman ginin, Wacce ta kama wajen shaguna uku.’

Sai dai kuma sun ce ‘ suna fargabar Inda wutar zata tsayar, domin kuwa a gefen shagunan wurin da ake dura gas.

Freedom Radio ta rawaito cewa sai zuwa lokacin da aka wallafa wannan labari hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano ta karasa wurin, yayin da ‘yan Sanda tuni suka Isa wurin.

Rahoton: Shamsiyya Farouk Bello

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!