Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: An ci tarar dubu 50 ga ƴan kasuwar Tumatir a Sabon Gari

Published

on

Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta yankewa ƴan kasuwar Tumatir da ke Sabon Gari tatar Naira dubu 50 sakamakon karya dokar tsaftar muhalli.

Mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ne ya yanke tarar sakamakon samun kasuwar a buɗe tana ci.

Baya ga haka ma an samu kasuwar da rashin tsafta wanda hakan ne ya sanya aka yi sammaci shugabannin ta.

Kotun ta buƙaci shugabannin kasuwar da su je ma’aikatar muhalli domin amsa tambayoyi kan tuhumar da ake yi musu.

Da yake jawabi bayan duban Tsaftar Muhalli, Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, gwamanatin Kano ba za ta lamunci karya doka ba, wadda kuma za ta iya cutar da Al’ummar da basu ji ba, ba su gani ba.

Yayin duban Tsaftar muhalli na ƙarshen wata a ranar Asabar an ci tarar masu ƙananan sana’o’i da su karya doka, sai dai an yabawa matuka baburan adaidaita sahu bisa yadda suka bi doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!