Connect with us

Labaran Wasanni

Yanzu -yanzu an dage gasar wasanni ta kasa saboda barazanar Corona

Published

on

Ministan matasa da wasanni na kasa  Mista Sunday Dare, ya sanar da dage gasar wasanni ta kasa  ‘National sport Festival’ karo na 20, da za ta  gudana a birnin  Edo na jihar Benin a shekarar bana  sakamakon barazanar cutar Coruna.

Ministan ya bayyana haka ne  a shafin sa na sada zumunta na twitter , in da yace bayan  wata tattaunawa da yayi da kwararru da ministan lafiya, da duba yanayin da cutar mai taken Covid 19, ke yaduwa  sakamakon barazana yasa aka yanke shawarar dage wasannin. Ya kuma kara da cewa za  a sanar da matsaya ta gaba dangane da gasar a gaba.

Minista Dare, ya kara da cewa  an yanke shawarar bayan tuntubar shugaban kasa tare da yi masa bayanai wanda sukayi shi da ministan lafiya, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da dage gasar gaba daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,104 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!