Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kano Pillars ta lallasa Jigawa Golden Stars

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta samu maki uku na galaba akan abokiyar burminta Jigawa Golden Stars da ci biyu da nema a gasar wasan firimiya ta kasa da yammacin yau.

Wasan na mako na ashirin da hudu an buga shi ne a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.

Dan wasan Kano Pillars Auwalu Ali Malam, shi ya zura kwallaye guda biyu a mintuna na 29 da bugun daga kai sai mai tsaron gida, sai na 62 a zagaye na biyu bayan hutun rabin lokaci.

Da yake jawabi ga manema labari jim kadan bayan tashi da ga wasan Auwalu Ali Malam wanda aka zaba a matsayin dan wasa mafi hazaka na wasan, yace fatan sa a gasar kakar wasa ta bana ya zama dan Kwallon da ya fi kowa yawan kwallaye a raga.

A ta bakin mai horar da kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars, Ibrahim Musa Jugunu, ya yi kira ga ‘yan Kwallo da su kara hakuri, tare da shan alwashin samun maki uku akan Wikki Tourist a garin Bauchi, a wasa na gaba na mako 25 da zasu fafata a can.

Zuwa yanzu haka dan wasa Auwalu Ali Malam da takwaran sa na Akwai United Ndifirike Effiong, suke Jagorantar  zura kwallaye mafiya yawa in da kowannen su ke da kwallo sha daya.

Karin labarai:

Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu

Kano Pillars ta lallasa Delta Force da ci 6-1

Sauran wasannin da aka fafata sun hada da:

Plateau United 2-1 Nassarawa United.

Amos Gyang 27’ (PEN), Ibrahim Mustapha 82’ – Chinedu Ohanachom 40’

Kano Pillars 2-0 Jigawa GS

Auwalu Ali 29’ (PEN), 62’

FC Ifeanyiubah 2-1 Dakkada

Samuel Kalu 2’, Uche Onuoha 25’ – Eso Archibong 71’ (PEN)

Kwara Utd 1-0 Wikki

Chinedu Ufere 82’

Enyimba 3-0 Sunshine Stars

Martins Usule 12’, Stanley Dimgba 59’, Dare Olatunji 90+2’

Katsina Utd 1-1 Akwa Utd

Suleiman Ibrahim 84’ – Ndifreke Effiong 8’

Rangers 1-0 Rivers Utd

Chinonso Eziekwe 39’

Heartland 2-0 Lobi

Pascal Eze 42’, Chukwuemeka Obioma 69’

Wolves 2-0 MFM

Michael Okoyoh 89’, Charles Atshimene 90’

Abia Warriors 2-1 Adamawa Utd

Yakub Hammed 46’, Fatai Abdullahi 90+5’ (PEN) – John-Paul Chinedu 45’.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!