Connect with us

Labaran Wasanni

Yanzu-yanzu: Dan wasan kungiyar Enugu Rangers ya Mutu

Published

on

Dan wasan Kwallon kafa na kungiyar Enugu Rangers International, Ifeanyi George, mai wasa a tsakiya ya rasu sakamakon hadarin Mota da ya rutsa dashi da abokanan sa su biyu a safiyar yau.

Dan wasa Ifeanyi George , na kan hanyar sa ta zuwa Lagos daga jihar Enugu, da niyyar yin hutu bayan dakatar da gasar Firimiya ta kasa, sakamakon bullar Cutar Corona Virus da barazanar yaduwar ta.


Motar da dan wasan ya ke ciki tare da abokanan nashi tayi taho mu gama da Babbar motar daukar kaya, ta Kwantina wanda a nan take dan wasan da abokanan shi suka rasu.

Wannan shi ne karo na biyu kasa da wata daya ,da wani dan wasa ya rasu da suke buga gasar Firimiya ta kasa, bayan mutuwar dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Nassarawa United Chineme Martin’s, a baya baya nan sakamakon taho mu gama da buguwa a kai da yayi wanda ya Mutu nan take a cikin fili kan a kai zuwa ga Asibiti.

Karin labarai:

Yanzu-yanzu: Dan wasan Nasarawa Utd ya mutu ana tsaka da wasa

Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,751 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!