Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kocin Arsenal ya kamu da cutar – Corona

Published

on

Hukumar shirya gasar premier ta kasar Ingila ta tabbatar da cewa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya kamu da cutar Corona.

A yammacin jiya ne dai hukumar shirya gasar premier ta Ingila ta tabbatar da kamuwar mai horarwar ta Arsenal.

Hakan ya sanya aka rufe filin daukar atisaye na kungiyar kwallon kafar ta Arsenal mai suna Colney training center  da ke birnin London sakamakon samun mai horar da kungiyar ta Arsenal dauke da cutar ta Covid-19.

A ranar Asabar din nan ne dai kungiyar kwallon kafar ta Arsenal za ta yi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Brighton.

Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko za a ci gaba da wasanni a gasar ta firimiya a wannan mako kamar yadda aka sara tun da farko

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!