Labarai
Yanzu-yanzu: An yi sulhu tsakanin Abba Kabir da Shiekh Aminu Daurawa
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi sulhu tsakanin sa da babban kwamandan hukumar Hisba Shiekh Aminu Ibrahim daurawa.
A daren ranar Litinin ne tawagar Malamai daga ƙungiyoyi daban daban suka raka Shiekh Daurawa zuwa fadar Gwamnati.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an yi doguwar tattaunawa ta tsawon awa guda, kafin a kai ga sulhunta shugabannin biyu.
Tuni dai Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ya amince da komawa bakin aikin aikinsa, domin ci gaba da jagorantar hukumar Hisba.
Idan za a iya tunawa a ranar Juma’a ne aka wayi gari da ganin faifan bidiyon Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda a ciki ya sanar da ajiye muƙamin sa na babban kwamandan hukumar Hisba.
Matakin nasa na zuwa ne kwana guda biyo bayan wasu kalamai sa gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ga me da yadda hukumar Hisba ke tafiyar da ayyukan ta.
Kuma sulhun ya samu nasara ne bayan da ɓangaren zauren haɗin kan Malamai da ƙungiyoyin Musulunci na Jihar Kano suka bibiyi abinda ya faru tare da yin tsayin daka wajen kamo bakin zaren.
You must be logged in to post a comment Login