Labaran Kano
Yanzu-yanzu: Ganduje zai gabatar da kasafin kuɗin 2022
Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zauna a zauren majalisar dokokin Kano domin gabatar da kasafin kuɗin 2022.
Gwamnan ya isa majalisar tare da rakiyar ƴan majalisar zartaswar jihar Kano da misalin ƙarfe 10:01 na safiyar ranar Alhamis 28 Oktoba, 2021.
Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya gabatar da wasiƙar da gwamnan ya aike mata domin sanar da zuwansa a wannan rana, don gabatar da kasafin.
Ku ci gab ada bibiyar mu don jin yadda za ta kasance.
You must be logged in to post a comment Login