Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta naɗa sabon sarkin Gaya

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta naɗa sabon sarkin Gaya.

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya Amince da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a Matsayin Sabon Sarkin Gaya Mai daraja ta ɗaya.

Sakataren gwamnati kuma wazirin Gaya Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da naɗin a ranar Lahadi.

Amincewar hwamnan ta biyo bayan shawarar sunaye uku da masu naɗa sarki a masarautar suka gabatar kana daga baya aka amince da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim a matsayin sarkin na Gaya.

Wannan dai biyo bayan rasuwar Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulƙadir a ranar Laraba bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Tuni dai gwamnatin Kano ta yi addu’ar samun jagoranci na gari ga sabon sarkin cikin ayyukan da zai gudanar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!