Labarai
Yanzu-yanzu : Matasa na zanga-zanga a Katsina
Wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihar Katsina inda suka tare hanyar da ta haɗa garin Jibiya zuwa birnin Katsina sakamakon yadda ƴan bindiga ke ci gaba da kai masu hare-hare.
Sama da mutanen garuruwa goma ne suka haɗu wajen zanga-zangar wadda rahotanni suka ce ta haddasa mutuwar wani matashi wasu da dama kuma suka jikkata a cewar wani ganau da ya shedawa wakilin Freedom Radiyo Yusuf Ibrahim Jargaba a Katsina.
Kakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina SP Isa Gambo, ya tabbatar da zanga-zangar yana mai cewar suna nan suna ƙoƙarin shawo kan masu al’amarin kuma nan gaba kadan za su fitar da cikakken bayani a kai.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da al’umma ke yin zanga-zanga a jihar ta Katsina kan matsalar tsaro da ya addabe su.
A ya yin da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin sa za ta tattauna da mutanen da ake zargi da kai hare-hare da satar mutane domin karbar kudin fansa don kawo karshen matsalar tsaro da take addabar jihar.
An dai jiyo daraktan yada labaran gwamnan jihar, Audu Labaran, na shedawa manema labarai cewa wannan bashi ne karon farko da gwamna Masari ke cewa zai shiga daji domin tattaunawa da masu kai hare-haren a Katsina
daraktan yada labaran na fadin hakan ne a ya yin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da aka yi a fadar gwamnatin ta Katsina a kwanakin baya.
You must be logged in to post a comment Login