Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu- Motar dakon kaya ta fadi a gadar Watari

Published

on

Wata babbar motar dakon kaya ta fadi a gadar watari da ke kan titin Gwarzo.

Motar mai dauke da raftan takalma ta taso daga cikin garin Kano da yammacin Asabar din nan.

Tun da fari dai gangar jikin motar ya tsinke daga jikinta tare da faduwa a tsakiyar titin lamarin da yayi sanadiyyar rufewar ta.


Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Freedom Redio cewa suna cikin tafiya sai kawai suka ji ya matse su a tsakiyar gadar.

 

A cewar direban wata motar gida mai suna Rabi’u Lawan ya ce, “muna cikin tafiya a jere da babbar motar kawai sai muka ji ya matse mu da jikin gadar kafin mu ankara kuma gangar jikin motar ya tsinke daga jikinta ya fado a tsakiyar titin”

Faduwar motar dai ya janyo cunkoson ababen hawa a hanyar, lamarin da ya sanya masu ababen hawa fantasma cikin kwazazzabai don wucewa yayin da wasu suke juyawa don sauya hanya.

Tuni dai jami’an Yan sanda da ke yankin suka yi wa wajen kawanya don shawo kan lamarin.

Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa babu wanda lamarin ya shafa, Sai dai tuni aka nemi direban motar aka rasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!