Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Yanzu Yanzu Nasir El Rufa’i ya ziyarci tsohon sarkin Kano a Awe

Published

on

Wani rahoto da ga jaridar Daily Trust , ya  tabbatar da cewa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i, ya ziyarci tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi , a gidan da aka kai shi  zama dake garin Awe, na jihar Nassarawa da safiyar yau Alhamis.

Rahotannin sun tabbatar da cewa , gwamnan ya je ziyarar ne don  ganin halin da sarkin yake ciki tare da ganawa da shi,  wanda hakan ya sa shine gwamna na farko da ya kai ziyara  ga tsohon sarkin bayan tumbuke shi daga mulki da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin din makon da muke ciki.

Labarai masu alaka.

Tawagar jami’an tsaro na rakiyar fita daga fada ga Sarki Sunusi

An nada Sarkin Bichi Sabon Sarkin Kano

A baya dai wasu sarakuna na jihar Nassarawa, sunyi kokarin ziyartar tsohon sarkin amma jami’an tsaron da  aka girke da ke lura da shi, suka hana su shiga wajen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!