Labaran Kano
An nada Sarkin Bichi Sabon Sarkin Kano
A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya fitar mai dauke da sa hannun sa, ta tabbatar da cewa Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero, ya zama sabon Sarkin Kano, jim kadan bayan tsige Muhammadu Sunusi na II a yau Litinin.
Sanarwar ta kara da cewa masu ruwa da tsaki wajen nadin sarautar ta Sarkin Kano sun amince da nadin nan take a fadar gwamnatin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login