Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Wani magidanci ya hallaka kansa a Kano

Published

on

Wani magidanci mai suna Ibrahim Abubakar da ke sana’a a titin gidan Zoo ya rataye kansa.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, kuma kafin a kawo masa ɗauki har ya rasa ransa.

Ɗan marigayin mai suna Abdussalam Ibrahim ya shaida wa Freedom Radio cewa, tare suka yi sallar la’asar da mahaifin.

Amma yana komawa shagon sai ya tarar ya rataye kansa.

A cewar Abdussalam ya ce, “Mahaifin nasa yana fama da lalurar ƙwaƙwalwa, sannan yana cikin halin rashi ga shi kuma auren ƴarsa ya matso”.

Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce, zai bincika lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!