Manyan Labarai
Yaran Jahar Kano: Me yasa Buhari bai magantu da wuri ba?
Tun lokacin da bayanai suka fita a kafafan sadarwa da kafofin yada labaran kasar nan na yanar gizo na sace yaran jahar Kano, kungiyoyin addini suka fara magantuwa akan sace yaran na Jahar Kano zuwa jahar Anambra domin mai da su kirista.
Duk da maganganun da aka rika yi na kiraye kirayen alúmma su yi magana domin kwato hakkin yaran ‘’yan asalin jahar Kano, wanda alúmmar jahar Kanon suka damu da rashin yin maganar tasa shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ita dai fadar shugaban ta Najeriya ba ta fitar da matsayar ta akan sace yaran Kano din guda tara ba ,har sai da aka kai kwanaki takwas da fallasar wannan lamari .
Jamaa da dama dai suna ganin jahar Kano itace cibiyar siyasar shugaba Muhammadu Buhari, inda suke ta dakon suga ya magantu game da sace yaran na Jahar Kano, amma hakan ta faskara har sai bayan kwanaki takwas.
Kungiyoyi irin su Muslim rights concern wacce Farfesa Ishaq akintola ke shugabanta itace kungiyar Musulmin Najeriya ta farko da ta fara fitar da matsayinta ,sannan tayi tir da dabi’’ar wasu daga cikin kabilar Igbo na kasar nan da suka sace yaran Kano tare da sayar da su.
Sai daga baya kungiyoyi suka rika biyowa irin su kungiyar kabilar Igbo ta jahar Kano inda ta nesanta kanta daga wadanda suka sace yaran na jahar Kano .
Ita ma kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jahar Kano ,tayi tir da lamarin inda tace wadanda suka sace yaran na Jahar Kano ba kiristoci bane kuma basu da alaka da tanade tanaden addinin kirista.
Matsin lambar da fadar shugaban kasar ta fuskanta a kafafan sada zumuntar ya jawo cecekuce tsakanin wasu daga cikin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari da sauran alúmma.
Shi dai shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai, farin jini a jahar ta Kano tun daga ranar da ya shiga siyasa ya yanki katain tsohuwar jamiyyar APP a mazabar sa ta Daura ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2002.
Duk zabukan da shugaba Muhammadu Buhari ya rika tsayawa duk da zargin tafka magudi da aka ce anyi a zabukan kasar nan, shugaban bai taba faduwa zabe a jahar Kano ba.
Wannan dalili ne ya sa masana suke ganin cewa a tarihin siyasar shugaba Buharin, bashi da garin da ya wuce jahar Kano da zai kira ta a matsayin cibiyar siyasa.
Ko jamiyyar CPC da shugaban yayi mata takara a shekarar 2011 , sai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kayar da takwaransa a takarar shugaban kasa kuma Gwamnan jahar Kano mai ci na wancan lokaci, wato Malam Ibrahim shekarau na jamíyyar ANPP.
Tun dai sanda shugaban kasar ya dare karagar mulkin Najeriya a shekarar 2015 , alúmmar ta jahar Kano suke ganin kamar shugaban yana ko in kula da lamarin su, duk da cewa itace jahar da tafi rabauta da mukaman Gwamnatin tarayya masu gwabi gwabi daga yankin arewacin kasar nan.
Kwanaki takwas da fadar shugaba Buhari ta dauka bata ce komai ba akan sace yaran na jahar Kano ya matukar tunzura wasu daga cikin alúmma har suke ganin ko shin shugaban ya damu dasu.
Ko a zaben shekarar bana al ‘ummar ta jahar Kano basu kwayewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya ba, inda suka sake afka masa kuriu fiye da miliyan daya kamar yadda suka saba ,ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar ta 2019.
Shin ko laifin waya wajen jan kafa na fitar da bayanan shugaban kasa musamman ma idan ya shafi alúmmar jahar Kano ?