Labarai
A ranar Litinin ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko suka cika kwana 85 a hannun ƴan bindiga
A ranar Litinin ne ɗaliban makatantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke jihar Neja ke cika kwanaki 85 a hannun masu garkuwa da mutane.
A ranar 30 ga watan Mayun wannan shekara ne, ƴan bindiga suka kai hari makarantar inda suka yi garkuwa da ɗalibai 136 da
har kawo yanzu ba a kai ga ceto su ba.
Da take tsokaci a kai, gamayyar ƙungiyoyin Arewacin ƙasar nan ta Coalation of Northern Groups wato CNG ta bayyana takaicinta, harma kwamared Abdul’azizi Sulaiman mai magana da yawun ƙungiyar, ya ce “abin damuwa ne ƙwarai yadda hukumomi suka gaza ceto ɗaliban”.
A cewarsa, “babu Gwamnan da zai bar ɗansa yayi kwana goma a hannun ƴan bindiga, amma ga ƴaƴan talakawa sun doshi kwana ɗari”.
You must be logged in to post a comment Login