Rahotonni
Abubuwan da ya kamata ku sani game da ranar masana harhada magunguna ta duniya
Kungiyar masana kimiyyar harhada magunguna ta kasa ta sha alwashin tallafawa gidajen marayu da masu fama da lalurar kwakwalwa da magunguna don inganta lafiyarsu.
Sakataren kunggiyar Kwamared Rabi’u Abu Tandama ne ya shaida hakan a yau, jim bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, wanda ya mayar da hankali kan ranar ilimin kimiyyar hada magunguna ta duniya ake gudanarwa yau, wanda Majalisar dinki duniya ta ware.
Ya kuma da cewa akwai shirye- shirye da dama da suka tsara gudanarwa a wannan rana don tunawa da bikin a nan Kano.
A na ta bangare Shugabar mata ta kungiyar reshen Kano Ayat Uba Adamu, kira ta yi ga iyaye da su rinka barin ‘ya’yansu mata suna shiga harkokin karatun da suka shafi kimiyya, musamman ma na aikin hada magunguna.
Taken bikin na bana dai shi ne dacewar mai ilimin kimiyyar hada magunguna a duniyar magani.