Labarai
Yau ake cika shekara daya da mutuwar Umar Sa’idu Tudun-Wada
Tsohon Mataimakin shugaban rukunin tashoshin freedom rediyo, Mallam Umar Saidu Tudunwada, ya rasu a ranar 30 ga watan Yunin 2019.
Marigayi Tudunwada ya rasu ranar Lahadi daga kan hanyarsa ta komawa Kano daga Abuja, bayan da ya halarci wani taron kungiyar kafafen yada labarai.
Tsohon mataimakin shugaban rukunin gidajen rediyon na freedom, ya yi hatsarin mota ne a yankin karamar hukumar Kura ta jihar Kano.
Marigayi Umar Said Tudun wada ya dauki shekaru yana matsayin Janar Manaja na gidajen rediyon Freedom, inda daga bisani ya kasance daraktan yada labaran tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.
A yau ne aka gudanar da taron addu’o’i na tunawa da marigayin a dakin taro na fadar gwamnatin Kano,wato Coronation Hall.
ya rasu ya bar mata 3 da yaya da jikoki da dama.
You must be logged in to post a comment Login